Get Mystery Box with random crypto!

SHAWARA GUDA 7 KAN KUƊI 1. Ka nemi kuɗi nema na gaske, kada | Sheikh Ahmad Tijjani Guruntum

SHAWARA GUDA 7 KAN KUƊI

1. Ka nemi kuɗi nema na gaske, kada ka taɓa saka wasa a neman kuɗi, matsaloli da yawa idan ka samu kuɗi za su warware.

2. Idan ka na da iyaye kada ka yarda wani ya fi su more kuɗinka, kamar yanda su ka kasance sanadin zuwanka duniya haka nan su ne sanadin arzikinka.

3. Idan ka samu kuɗi ka riƙa kyauta, musamman ga mabukata, mutane da yawa ba sa samu ne saboda ba sa bayarwa.

4. Ka tabbatar ka na da aminan da za su iya ba ka bashi mai kauri, wato sun yarda da kai kuma su na da kuɗin, duk ranar da kuɗinka ya gaza ma ka rana za su yi ma ka.

5. Kada ka ci bashi sai kan abunda ya zama dole, sannan kafin ka ci ka tabbatar ka tsara yanda biyan kuɗin zai samu, da yawan mutane sun yi asarar mutunci saboda kin biyan bashi sun kuma talauce saboda cin bashin da ba za su iya biya ba.

6. Idan har ka samu kuɗi, bakinka ya shaida, wato ka ci mai kyau ka sha mai kyau, rashin cin mai kyau na illata lafiya da jiki.

7. Ka tabbatar ka na yawan sanya sabbin huluna, su na taimakawa wajen kiyaye mutunci, cikar kamala da bayyana ado.

https://t.me/zaurendaawaTV

Barka da safiya.