Get Mystery Box with random crypto!

Sheikh Ahmad Tijjani Guruntum

Logo saluran telegram sheikhahmadtijjaniguruntum — Sheikh Ahmad Tijjani Guruntum S
Logo saluran telegram sheikhahmadtijjaniguruntum — Sheikh Ahmad Tijjani Guruntum
Alamat saluran: @sheikhahmadtijjaniguruntum
Kategori: Agama
Bahasa: Bahasa Indonesia
Pelanggan: 29.05K
Deskripsi dari saluran

Fadakarwa,Ilimantarwa,Wa'azantarwa etc👳

Ratings & Reviews

3.00

2 reviews

Reviews can be left only by registered users. All reviews are moderated by admins.

5 stars

0

4 stars

1

3 stars

0

2 stars

1

1 stars

0


Pesan-pesan terbaru

2024-05-14 15:47:02 RIƘE AMANAR AURE SAI GWARZO


Tare da: Professor Mansur Isa Yelwa (Hafizahullah)

Zaku Iya Samun Cikakken Wannan Video ta wannan Link dake Ƙasa:

.



Karku manta ku danna mana a Subscribe domin samun short videos na Malam da zaran an ɗaura.

06/11/1445 A.H
6.1K views12:47
Buka / Bagaimana
2024-05-14 12:37:30 UPDATE GAME DA TAPSWAP!

Tapswap sunzo da sabbin Task Wanda idan kayisu zaka samu Tapswap guda 1,800,000 (1.8 Million).

Sede a yanzu idan ka shiga Tapswap dinka bazaka ga wadannan Task din ba, amma meyasa? dalili kuwa an cire 'yan Nigeria daga cikin wanda zasu iya yin task din.

Hanyar da zaku bi cikin sauki kuyi wannan task din, shine kuyi amfani da VPN musanman "Tunnel Bear" ko waninsa idan baku dashi Application ne zaku iya dakko wa A Play store.

Bayan kun shiga Application din VPN din se kuyi Connecting da kasar Germany se Ku shiga Tapswap dinku zakuga wajen task yasa alamar Ja, se Ku shiga kuyi nan take zaku samu points 1.2 Million.

Na Biyun shi kuma idan kun gama da na daya se Ku fito daga Tapswap din, sannan Ku koma Application dinku na VPN se kuyi connecting da United State se Ku koma Tapswap dinku kuna shiga zaku kuma ganin sabbin task se kuyi.

Kuje kuyi zaku godemin.

Share with your friends and earn bonuses for each friend you invite and for their activity:

Your referral link:https://t.me/tapswap_mirror_bot?start=r_1244022388

Please Share with others...!

5.4K views09:37
Buka / Bagaimana
2024-05-13 13:43:27 NIGERIA KASHIN DANKALI


Tare da: Malam Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum (Hafizahullah)

Zaku Iya Samun Cikakken Wannan Video ta wannan Link dake Ƙasa:

.



Karku manta ku danna mana a Subscribe domin samun short videos na Malam da zaran an ɗaura.

05/11/1445 A.H
5.4K views10:43
Buka / Bagaimana
2024-05-13 08:40:21 ZIKIRIN SAFE DA MARAICE

حَسْبِيَ اللَّهُ لاَ إِلَهَ إِلاَّ هُوَ عَلَيْهِ تَوَكَّلْتُ وَهُوَ رَبُّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ. (سبع مَرّات)

Hasbiyal-lahu la ilaha illa huwa, 'alayhi tawakkalt, wahuwa rabbul-'arshil-'azeem (7)

Allah ya ishe ni, babu abin bautawa da gaskiya sai Shi. A gare Shi kadai na dogara, shi ne Ubangijin al'arshi mai girma (sau bakwai da safe da maraice).

Wanda ya karanta ta kamar yadda aka ce, Allah zai yaye masa duk abin da ya dame shi na al'amarin duniya da na lahira.

Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Duk musulmin da ya karanta wannan addu’ar sau bakwai da safe, sau bakwai da yamma, to Allah zai azurta shi da abin da ya isar masa da dukkan damuwarsa.

Muna sane da cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Shi, don haka mu fayyace dalilin da ya sa ya ishe mu, kamar yadda ya mallaki sifofin da suka sanya shi ya cancanci a bauta masa.
Kamar yadda Allah ya isar mana, bangaren addu’a na gaba shi ne bayyanar da sanin haka, wato mu dogara gareshi shi kadai wato muna da Tawakkul gareshi.

Domin mu kara tabbatar da dalilin da ya sa muka dogara gare shi, muna tunatar da kanmu girmansa, domin shi ne Ubangijin Al'arshi mai girma. An siffanta darajarsa a cikin tafsirin Ayatul Kursiy.

Wannan addu'ar tana tafe ne a kan Tawakkul ga Allah, kuma ita ce kadai daya daga cikin addu'o'in da za a yi sau bakwai.

Watakila wannan ya faru ne saboda muhimmancin Tawakkul, da cewa ba abu ne mai sauki ba don haka sai mutum ya yawaita addu'a don tabbatar da ma'anoni sun tabbata a cikin zuciyarsa.

A lokacin da Allah ya so ya ambaci manyan halayen muminai a cikin suratu Anfal, sai ya hada da ingancin Tawakkul dinsu a gare shi.

Tawakkul yana kawo fa'idodi masu yawa. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Idan kuna da Tawakku ga Allah yadda ya kamata, da Ya azurta ku kamar yadda Ya azurta tsuntsaye. Shin, ba ka gani ba, da sassafe suke fita da tare da sun mallaka komai ba kuma su koma a koshe a rana?”.

Abu Dawud ya ruwaito hadisi na 5081
Qur'an, Surah Al-Anfal [8:2-4]
Tirmiziy ya ruwaito hadisi na 2344 da Ibnu Majah hadisi na 4164.
Hadisi ya tabbata a cikin Sahihul Bukhari, hadisi na 6472, da Sahih Muslim hadisi na 220.
'Mukhtasar Minhaj Al-Qasideen' na Ibn Qudamah Al-Maqdisi
Hadisi ya tabbata a cikin Sahihul Bukhari, hadisi mai lamba ta: 4563.
5.2K views05:40
Buka / Bagaimana
2024-05-06 18:59:13 *WA'AZIN WALIMAN AURE*


Tare da: _Malam Ahmad Tijjani Yusuf Gurumtum da Professor Mansur Isa Yelwa_

Wannan shine Muhadarar da Malaman suka gabatar jiya Lahadi 05/May/2024 a Masallacin Anas Bin Malik dake nan cikin garin Bauchi.

https://youtube.com/live/QI15_kzBybo

https://t.me/zaurendaawaTV

Ayi Sauraro Lafiya
5.9K views15:59
Buka / Bagaimana
2024-05-06 18:04:14 YADDA AKE ZAMAN AURE A MUSULUNCI


Tare da: Malam Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum (Hafizahullah)

Zaku Iya Samun Cikakken Wannan Video ta wannan Link dake Ƙasa:

.



Karku manta ku danna mana a Subscribe domin samun short videos na Malam da zaran an ɗaura.

27/Shawwal/1445 A.H
6.4K views15:04
Buka / Bagaimana
2024-04-30 16:18:17 Zuwa gare ku Maza

Duk kishin ka matuqar bai sa ka................

Kare mutunci da kimar iyalan ka ba, kishin da bai sa ka kyautatama iyalanka ba, kishin da bai sa ka sauqe hakkokin su da ke kan ka ba, kishin da bai sa ka rufe musu hanyoyin da zai kai su ga halaka ba, kishin da bai sa ka bi kadun su in da suke da gaskiya ba, kishin da bai sa ka kyautata hali da mu'amalar ka ga iyalan ka ba....................

Tabbas wannan ba kishi bane face son zuciya da qarancin tsoron Allah da rashin sanin menene kishi, da rashin sanin darajar kan ka da na iyalan ka, da rashin sanin menene aure, manufar aure da yadda ake zaman sa.

Duk namijin da yasani kuma ya kiyaye wannan shi ne me asalin kishin iyalan sa ba mai tozarta iyalan sa ya quntata musu, ya bar su cikin buqata kuma ya gujema dawainiyar sa ba.

https://t.me/zaurendaawaTV
8.8K views13:18
Buka / Bagaimana
2024-04-25 12:54:34 سبحان الله
SubhanAllah

الحمد لله
Alhamdulillah

لا إله إلا الله
La ilaha illa Allah

الله أكبر
Allahu Akbar

أَسْتَغْفِرُ اللّٰهَ
Astaghfirullah

لاَّ إِلَـهَ إِلاَّ أَنتَ سُبْحَـنَكَ إِنِّى كُنتُ مِنَ الظَّـلِمِينَ
La ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minaz zalimi
10.9K views09:54
Buka / Bagaimana
2024-04-22 13:44:48 SHAWARA GUDA 7 KAN KUƊI

1. Ka nemi kuɗi nema na gaske, kada ka taɓa saka wasa a neman kuɗi, matsaloli da yawa idan ka samu kuɗi za su warware.

2. Idan ka na da iyaye kada ka yarda wani ya fi su more kuɗinka, kamar yanda su ka kasance sanadin zuwanka duniya haka nan su ne sanadin arzikinka.

3. Idan ka samu kuɗi ka riƙa kyauta, musamman ga mabukata, mutane da yawa ba sa samu ne saboda ba sa bayarwa.

4. Ka tabbatar ka na da aminan da za su iya ba ka bashi mai kauri, wato sun yarda da kai kuma su na da kuɗin, duk ranar da kuɗinka ya gaza ma ka rana za su yi ma ka.

5. Kada ka ci bashi sai kan abunda ya zama dole, sannan kafin ka ci ka tabbatar ka tsara yanda biyan kuɗin zai samu, da yawan mutane sun yi asarar mutunci saboda kin biyan bashi sun kuma talauce saboda cin bashin da ba za su iya biya ba.

6. Idan har ka samu kuɗi, bakinka ya shaida, wato ka ci mai kyau ka sha mai kyau, rashin cin mai kyau na illata lafiya da jiki.

7. Ka tabbatar ka na yawan sanya sabbin huluna, su na taimakawa wajen kiyaye mutunci, cikar kamala da bayyana ado.

https://t.me/zaurendaawaTV

Barka da safiya.
11.2K views10:44
Buka / Bagaimana